Dakarun Najeriya sun kashe sama da yan Boko Haram Dari tare da kwace makaman su Arewa maso gabas
Read Time:37 Second
Hukumar Sojojin Najeriya sun ce Dakarun ta dake karkashin operation lafiya dole sun kashe da yan Boko Haram Dari a karkade su raguwar su a yankin Arewa maso gabas.Kakakin hukumar Sojojin Najeriya Birgediya janaral Sani kukasheka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar ranar litinin.
Yace dakarun dake cikin zumar yaki sun gudanarda aikin karkade sauran yan Boko Haram a mabuyar su dake Borno da Yobe. Kukasheka yace dakarun tare da samun goyon bayan Sojojin sama sun jiwa yan Boko Haram sosai harya kai da sun tura su zuwa Bakin tafkin Chadi.
Yace dakarun sun kashe yan ta’addan sosai tare da kwace bindigogi masu alburusai mai zafi a Giniri dake Yobe da Damasak, kross- Kauwa da Monguno a Borno.
