Mutane uku sun mutu, biyu sun ji ciwo yayinda magoya bayan Ganduje suka kara a Garin sa

Read Time:1 Minute, 3 Second

Akalla mutane uku aka kashe, biyu suka ji munmunar rauni a yayinda magoya bayan Gwamna Kano Abdullahi umar Ganduje suka kara da yan Adawa a garin sa Ganduje dake karamar hukumar Dawakin Tofa.

Lamarin ya faru ne ranar lahadi a lokacin da Ganduje ya tafi garin don halartan daurin auren wani daga cikin yan uwan sa. Wakilin mu ya gano cewa an fara rikicin ne a lokacin da magoya bayan jam’iyar Adawa suka fara masa ihu cewa Bama yi.

Lamarin da ya ingiza wasu Yan bangan siyasa dake cikin tawagar Gwamna Ganduje sai suka dauki makamai dake shake a cikin motar su, suka afkawa yan Adawa.Wani shaidan gani da Ido ya shaidawa kanfanin labarai na hotjist cewa ya ga gawa guda uku.

Da aka tuntube shi kakakin rundunar yan sanda na jihar Magaji majiya ya tabbatar da aukuwar lamarin.Sai dai kuma kakakin yan sanda yace mutum daya ne aka kashe, biyu da suka sami munmunar rauni suna wani asibiti da bai fadi sunan sa ba suna karban magani.

Yace duk wanda aka kama da hannun sa a rikiclafiyain zai gamu da fushin hukuma kuma rundunar yan sanda ba zata sake ta bar duk wanda ke kokarin kawo cikas ga zaman a Jihar a gabannin zabe na bana.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %