Yara uku sun mutu a wata gobara a Kano

Read Time:39 Second

A ranar litinin ne yara biyu suka mutu a sakamakon wata gobara da sanyin safiya a wani gida mai ciki biyu dake Sharada, ja’en yamma, cikin garin Kano. Kakakin hukumar kwana kwana na jihar Kano Alh saidu Muhammad ya shaidawa kanfanin dillancin labarai NAN cewa yaran da suka mutu mai shekara hudu da kuma bakwai.

Yace mun sami Kira daga wani Malam Bello Tukur da misalin karfe biyu da minti Tara na daren litinin cewa gobara ta kama wani gida.Daga samun labarin sai muka tura injin kashe gobara da misalin karfe biyu da minti goma Sha biyar don kashe gobarar.

Muhammad yace lokacin da wuta ta kama iyayen yaran sun ruga waje don Neman agaji daga makwabta amma duk kokarin da akayi na Ciro yaran ya ci tura.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %