Kano ta sami sabuwar jami’a mai zaman kanta irinsa na farko.

Read Time:33 Second

An kaddamar da wata sabuwar jami’a mai zaman kanta wacce ke da manufar yin bincike, kere kere da sana’oin hannu a birnin Kano.
Makarantar mai suna Skyline University Wanda ke da kayan zamani a jiya litinin ta fara taron wayad da kai ga sabbin dalibai data dauka kimanin 160.
Dayake magana da yan jarida shugaban makarantar furofesa Prana Krishna ya bayyana jami’ar wacce aka kafa a shekara ta 1990 a kasar daular larabawa a matsayin irin ta na farko a jihar.
Shugaban makarantar yace hukumar kula da Jami’oi na kasa ta amince da kwasa kwasai guda hamsin a jami’ar zata fara ne da dalibai 200 daga watan junairu na 2019.

Happy
Happy
0 %
Sad
Sad
0 %
Excited
Excited
0 %
Sleepy
Sleepy
0 %
Angry
Angry
0 %
Surprise
Surprise
0 %