Yan bindiga dadi sun kashe uban wata yarinya kana sukayi Garkuwa da ita a Katsina.
Read Time:18 Second
Wasu da ake zargin cewa yan bindiga dadi a ranar talata suka harbi Alhaji Nasiru Maimasara dake gidajen Gachi a karamar hukumar Kankia na jihar Katsina , bayan ya mutu sai suka kama yar sa dake kokarin guduwa.
Kakakin yan sanda na jihar Gambo isa ya tabbatar da aikuwar lamarin kana yace yan sanda na kokarin kamo yan bindiga dadin.
